Denmark da Tunisia sun tashi kurman duro a rukuni na hudu – BBC

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Denmark da ta Tunisia sun tashi ba ci a wasan farko a rukuni na hudu a Gasar Kofin Duniya da suka kara a filin Education City a Al Rayyan.
Duk da cewar Denmark ta saka 'yan wasa da yawa da ke buga Premier League, amma ta kasa doke Tunisia a wasan da suka yi ranar Talata.
Dukkan tawagogin sun ci kwallo amma rafli ya kashe, yayin da dan kwallon Denmark, Andreas Cornelius ya barar da dama mai kyau.
An samu tsaiko a minti na 95 lokacin da alkalin wasa, Cesar Ramos ya je ya duba talabijin kan laifin fenariti ga Denmark, amma daga baya alakalin ya tsaya kan hukuncin farko.
Denmark, wadda aka yi hasashen za ta iya lashe Kofin Duniya a Qatar na bukatar kara sa kwazo, idan har tana son taka rawar gani a wasannin.
A karon farko Christian Eriksen ya buga wa Denmark babbar gasar tamaula ta duniya, bayan da ya fadi kasa a cikin fili ana tsaka da wasa a Euro 2020.
Za a buga daya wasan rukuni na hudu tsakanin Faransa mai rike da kofi da Australia.

© 2023 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source