Mutum-mutumin Najeriya mai daraja da ya maƙale a Birtaniya – BBC

Asalin hoton, Woolley and Wallis
Ƴan sandan Birtaniya na ci gaba da riƙe wani mutum-mutumi da aka sace wanda kimarsa ta kai miliyoyin daloli.
Suna ci gaba da riƙe mutum-mutumin ne sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakanin dillalan kayayyakin tarihi na ƙasar Belgium da kuma wani gidan ajiye kayan tarihi na Najeriya kan batun mallakar mutum-mutumin, kamar yadda Barnaby Phillips ya rubuta.
Ranar 24 ga watan Janairun 2017 rana ce da aka yi sanyi kuma take cike da hazo a Landan.
Da tsakar rana, John Axford, wanda yana ɗaya daga cikin masu gwanjon kayayyaki na Woolley and Wallis, yana zaune a ofishinsa da ke a kasuwar Mayfair, yana jiran baƙo daga Belgium inda baƙon yake so ya nuna masa wani mutum-mutumi.
"Sai ya kawo wannan abin mai kyau," in ji Mista Axford.
Wani kan mutum-mutumi ne wanda aka yi shi da tagulla, wanda Mista Axford ya ce ya samo asali ne daga Ife da ke yankin Yarabawa a Najeriya.
Tun asali, kawunan mutum-mutumin na Ife, waɗanda aka yi su da tagulla, 20 ne kaɗai ake ganin suka rage a duniya, kuma sun kai kimanin shekara 700.
An yi su ne da ƙarfe kuma an yi amfani da kimiyya sosai wurin yin su kuma suna daga cikin mutum-mutumi mafi kyau da aka yi a Afrika.
"Irin wannan ba wai wanda ake sayarwa ba ne," in ji Mista Axford.
Amma mutum-mutumin yana da wani rami a gefen idonsa na hagu, wanda ya yi daidai da wanda aka ce hukumar kimiyya da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya Unesco ta bayar da rohoton cewa an sace.
"Sai na gane cewa muna da matsala," in ji Mista Axford.
"Idan da gaske ne, mutum-mutumin zai kai fam miliyan 20.
"Na shaida wa mutumin cewa wannan abu ne mai kyau, amma ba za mu iya sayar da shi ba. Dole mu ba ƴan sanda shi."
Asalin hoton, Woolley and Wallis
Sai mutumin ya tafi. Mista Axford, wanda yana tsoro ya bar mutum-mutumin ba a kusa da shi ba, sai ya yi barci da shi a gefen gadonsa.
Washe gari sai ya kai shi wurin ƴan sandan Birtaniya, waɗanda tun a lokacin suke riƙe da mutum-mutumin.
Domin bin wannan labari zuwa Mayfair, dole ne mu koma shekara 30 baya a birnin Jos da ke Najeriya.
A daren 14 ga watan Janairun 1987, ɓarayi suka shiga gidan tarihin Jos inda har aka yi wa ɗaya daga cikin masu gadin wurin duka.
Ɓarayin sun san me suke so – sai suka kwashi kayayyakin tarihi tara mafi muhimmanci da ke gidan tarihin sai suka tafi da su.
A shekarun 1980 da 1990, gidajen tarihi a Najeriya sun tafka asara matuƙa sakamakon fashin da aka rinƙa yi musu.
Wasu daga cikin ma'aikatan Hukumar Kula da Kayayyakin Tarhi ta Najeriya NCMM sun haɗa kai da wasu domin aikata satar kayayyakin.
Wata tsohuwar ma'aikaciyar hukumar ta shaida mani cewa ba shakka akwai haɗin bakin wasu ƴan cikin gida wurin aikata waɗannan sace-sacen.
Bayan nan ne NCMM nan take ta shaida wa Unesco abin da ke faruwa inda ta aika mata hotunan duka abubuwan da aka sace daga Jos.
A 1990, wani mai son sayar da wani mutum-mutumi na Benin ya tunkari wasu masu karɓar kayan tarihi a Switzerland domin sayar musu shi a kan rabin miliyan na kuɗin Swiss francs.
Sai mutanen suka soma tsoro inda da taimakon jami'an diflomasiyyar Switzerland da Najeriya da Amurka, sai aka gano cewa daga Jos aka sace shi inda aka mayar da shi Najeriya.
Sai dai sauran guda takwas ɗin dukansu sun ɓace.
Akasarinsu waɗanda suka haɗa da mutum-mutumin Ife, na daga cikin waɗanda aka lissafa a wani rubutu da Majalisar Kula da Gidajen Tarihi ta Ƙasa da Ƙasa ICOM ta yi a 1994 inda ta bayyana abubuwa ɗari da aka sace daga Afrika.
Sai dai bayan shekaru da dama wannan mutum-mutumin wanda aka sace aka gan shi a Belgium.
Asalin hoton, NCMM
A watan Nuwambar 2007, hukumomin Belgium sai suka shirya yin gwanjon wasu kayayyaki da aka ƙwace.
Cikin waɗanda aka yi gwanjon su har da mutum-mutumin Ife.
Wani dillalin kayan tarihi ne ya saye su kan euro 170. Haka kuma ya sayi wata garaya ma a wurin wannan gwanjon.
Irin wannan gwanjon da aka yi ya sa aka yi tambayoyi uku: ta yaya aka yi waɗannan kayayyakin tarihin suka shiga hannun hukumomin Belgium.
Me ya sa suka rabu da su; kuma shin dillalan sun san cewa za su sayi ɗaya daga cikin kayayyakin Afrika mafi girma?
Sai dai gwamnatin Belgium ta kasa yin ƙarin haske kan wannan lamari, sai dai ta ce ofishin mai shigar da ƙara da ke Ghent ya ƙaddamar da bincike kan lamarin.
Sai dai hukumomin Najeriya sun fusata sakamakon kasa amsa waɗannan tambayoyi da Belgium ta yi, zai iya sakawa ba zai taɓa yiwuwa Najeriya ta gano inda sauran kayayyakin da aka sace daga Jos suke ba.
Babatunde Adebiyi daga NCMM ya bayyana cewa batun Beligum ta kasa bayani kan me ya faru "abin dariya ne".
Ga dillalin kayan tarihin, na yi ƙoƙarin gano su. Na yi gajeruwar tattaunawa da su ta waya.
"Kun san cewa kayan sata za mu saya?" Haka na tambayi mutumin, wanda ba mu fadi sunansa ba.
"Ina ban sani ba, na sayi kayan ne daga hukumomin Belgium," in ji shi, sai ya ajiye wayar.
Asalin hoton, Anna Craven
Gidan tarihin Jos a shekarun 1970
Wannan labarin ya sake yin gaba zuwa shekara goma da suka wuce da kuma zuwa Landan a 2017, a lokacin da dillalin ya yi ƙoƙarin sayar da mutum-mutumin ta hanyar Woolley and Walllis waɗanda suka bayar da shi ga ƴan sandan Birtaniya.
A 2019, sai ƴan sandan suka ɗauki mutum-mutumin zuwa gidan tarihin Birtaniya, inda aka tabbatar da ingancinsa inda aka kwatanta shi da wanda aka yi a shekarun 1940.
"Sai na ji daɗi na asalin ne," in ji wani ƙwararre wanda ya ganshi.
Kafin haka, mutum-mutumin na nan ajiye a wani wurin ƴan sanda da aka ajiye shi sama da shekara biyar.
Me ya sa gwamnatin Birtaniya ba za ta mayar wa Najeriya da mutum-mutumin ba?
Ta nan ne wannan lamari ya dangana da batun shari'a.
Gwamnatin Najeriya ta tayar da wannan zance inda ta ce ita ke da wannan mutum-mutumin kuma ta shaida wa Gwamnatin Birtaniya bayan shaida wa ƴan sandan Birtaniyar.
"Kowa ya amince da cewa an sace wannan mutum-mutumin," in ji wani jami'in Birtaniya," amma shin dillalin ɗan ƙasar Belgium ya yi wani laifi ne nda ya saɓa wa shari'a? Ya saya ne daga hannun gwamnati."
Ƴan sandan Najeriya sun kafe kan cewa ba su da hannu a lamarin.
"Ba za mu iya ɗaukar wani abu daga wani ba," in ji wani jami'i.
"Wannan wani abu ne da Najeriya da kuma dillalin za su sasanta kansu."
A 2019, wata tawaga daga Najeriya ta je ta samu dillalin. Mista Adebiyi ya ce dillalin ya karɓe su.
"Na shaida masa cewa zai iya zama wani gwarzo a duniya.
Ya ce kuɗi yake so, ba wai mutane su rinƙa faɗin abubuwa masu daɗi game da shi ba," in ji Mista Adebiyi.
Ƴan Najeriya sun ce akwai wani lokaci da dillalin ya nemi a ba shi euro miliyan biyar, sai dai ya rage farashinsa.
A halin yanzu, hukumomin Birtaniya sun bayyana cewa yana neman fam 33,500.
A gajeruwar tattaunawar da muka yi ta waya, dillalin ya ce yana ta tattaunawa da ƴan Najeriya tsawon shekara uku kuma batun yin sasanci kan wannan lamari ya danganta ne daga ƴan Najeriyar.
Amma me ya sa Najeriya za ta biya idan za ta karɓi kayanta? "Mun bayar da rahoton ɓacewarsa a 1987. Ba za mu biya diyya ba," in ji Mista Adebiyu.
Wata mafita ɗaya da Birtaniya ta bayar ita ce kamar yadda gwamnatin Belgium ta yi gwanjon waɗannan kayayyaki a 2007, da su biya dillalin.
Gwamnatin Belgium ta ƙi cewa komai kan wannan lamari, amma ta ce mani sakamakon Najeriya ta kai Birtaniya a gaban hukumar Unesco domin shawo kan wannan matsala, za ta ci gaba da bayar da shawara kan su tattauna a tsakaninsu.
Na tambayi Mista Adebiyi kan cewa sakamakon yadda wannan mutum-mutumin yake da tsada ko ya kamata a sake mayar da shi gidan tarihin Najeriya.
"1987 ta sha bamban da 2022. Irin wannan satar ba za a iya yin ta a yanzu ba. An horas da jami'anmu fiye da baya."
A yanzu dai, wani jami'in Birtaniya ya jaddada mani cewa ana kula da mutum-mutumin Ife da ke ƙasar.
Barnaby Phillips, tsohon wakilin BBC ne a Najeriya kuma shi ya rubuta littafi kan kayayyakin tarihin da aka sace a Najeriya na Loot; Britain and the Benin Bronzes.
© 2023 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source